
Ministan babban birnin tarayya, Abuja Nyesom Wike ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2023, Alhaji Atiku Abubakar da kala masa sharri.
Yace Atiku ne yasa ake shirin bata masa suna da maganar cewa wai ‘ya’yansa sun mallaki filaye da yawa a Abuja.
Wike ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Lere Olayinka inda yace ‘ya’yansa kamar kowane dan Najeriya suna da ‘yancin mallakar filaye a ko ina suke so a fadin Najeriya.
Yace amma babu gaskiya a rahoton dake cewa, Ya baiwa ‘ya’yan Nasa filaye masu yawa a Abuja.
Wike ya kara da cewa, kamfanin Jordan Farms and Estates Limited kamfanine wanda ba mallakar ‘ya’yansa ba, wanda shine kamfanin da ake ta cece-kuce akan cewa an bashi filaye.
Ya kara da cewa, masu binciken kuma idan suna da hujjar cewa kamfanin na ‘ya’yansa ne su fito su fada.