Friday, July 17
Shadow

Mun Dauki jam’iyyar ADC dan amfani da ita wajan kayar da Gwamnatin Tinubu zabe a 2027>>Inji El-Rufai

Tsohon gwamna jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, gamayyar ‘yan adawa sun amince da shiga jam’iyyar ADC wadda zasu yi amfani da ita wajan kayar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zabe a shekarar 2027.

El-Rufai ya tabbatar da hakan ne a shafinsa na X sannan ya bayyana cewa, Sun baiwa tsohon ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola mukamin sakataren jam’iyyar na riko.

Aregbesola ya bayyana cewa ya amince da wannan mukami da aka bashi kuma jam’iyyarsu ta jama’ace a lokacin zabe da bayan zabe.

Karanta Wannan  Ina nan akan bakana, Bidiyon wannan yarinyar ba kuskure bane, kuma ba kaddara bace, gangancine, kuma dama can kilakice>>Inji Malam Muhammad bayan da aka yi kira gareshi ya tausasa harshe kan sukar Zulaihat

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *