Ga maganin Aljani kamar yanda yazo a Sunnar Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam).
Na daya shine a nemi tsarin Allah daga shaidan, Watau fadar A’udhu Billahi min al-Shaytan il-rajim.
Sulayman ibn Sard ya ruwaito cewa, wasu mutane na ta zage-zage a gaban Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) har fuskar daya daga cikinsu ta yi ja.
Sai Annabi Muhammad(Sallallahu Alaihi Wasallam) yace da mutumin zai fadi wasu kalmomi da abinda yake ji ya gushe, watau fadar ‘A’udhu Billahi min al-Shaytan il-rajim. (al-Bukhari and Muslim).
Karanta Falaki da Nasi.
Abu Sa’id al-Khudri Allah ya kara yadda dashi ya ruwaito cewa, Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance yana neman tsari daga sharrin mutum da aljani, amma bayan da aka saukar da Falaki da Nasi, sai ya koma karantasu ba tare da kari ba. (al-Tirmidhi, al-Nasai, Ibn Majah).
Karanta Ayatul Kursiyyu:
Karanta Ayatul Kursiyyu na hana Aljani zuwa kusa da mutum, musamman idan an zo kwanciya. (al-Bukhari).
Karanta Suratul Baqara:
Abu Hurayrah ya ruwaito cewa, Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace kada ku mayar da gidajen ku kamar makabarta, Kuma shaidan na guduwa daga gidan duk da ake karanta suratul Baqara.(Muslim).
Karanta Ayoyi biyu na karshen suratul Baqara:
Watau Amanarrasul….
Abu Mas’ud al-Ansari ya ruwaito cewa, Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace duk wanda ya karanta ayoyi biyu na karshen suratul baqara da dare sun isar masa. (al-Bukhari, Muslim).
Hakanan Al-Nu’man ibn Bashir ya ruwaito cewa, Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace idan aka karanta ayoyin karshen na suratul Baqara a darare 3, shaidan ba zai zauna a gidan ba. (al-Tirmidhi).
Karanta “La ilaha ill-Allah wahdahu la sharika lah, lahu’l-mulk wa lahu’l-hamd wa huwa ‘ala kulli shayin qadir” sau dari.
Abu Hurayrah ya ruwaito cewa, Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace duk wanda ya karanta “La ilaha ill-Allah wahdahu la sharika lah, lahu’l-mulk wa lahu’l-hamd wa huwa ‘ala kulli shayin qadir” sau dari. Za’a rubuta masa ladar ‘yanta bayi 10, za’a rubuta masa lada 100, za’a kankare masa zunubai 100, kuma za’a bashi kariya daga shaitan a wannan yinin har zuwa yamma, kuma babu wanda zai yi aiki me kyau fiye da abinda ya aikata sai wanda ya karanta fiye dashi.(al-Bukhari, Muslim)
Yawan Zikiri akai-akai, watau Ambaton Allah, Mutum zai iya rika karanta la’ilaha illallah, Subhanallahi, Walhamdulillah, Allahu Akbar.
Yawan zikiri na korar shedan inji Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam).
A yi kiran Sallah.
Abu Hurayrah ya ruwaito cewa, Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace idan shaidan ya ji kiran Sallah yana tserewa, dan haka a rika kiran sallah dan rabuwa da Aljani ko shedan.
A kuma rika karanta Qur’ani akai-akai. Kariyane daga shaidan.