Wednesday, January 15
Shadow

Maganin basir mai tsiro

MAGANIN BASIR MAI TSIRO DA YADDAR ALLAH.

السلام عليكم ورحمة الله وبركاته يا اكون

Muna yiwa kowa fatan alkhairi.

Juma_At_Kareem.

Wanda yake fama da basir ko da kuwa, basir din yayi tsiri yana fitar da jini ko Kuma ya kasance basir din, yana fitowa har sai an saka hannu an mayar da shi da ikon ALLAH ga wata fa’ida zan baku, in dai akan basir ne za a samu waraka in Sha Allahu.

Akwai masu cewa wai basir bashi da magani wannan maganar ba haka bane, babu wata cuta da Bata da magani Wanda ya sani ya sani Wanda bai sani ba bai sani ba.

Karanta Wannan  Amfanin ganyen magarya

Ana samo sassaken kanya da kuma ganyen sabara ga tana mun dora a hoto, ga wadanda basu santa ba.

Sai Kuma zuma Mai kyau sai a shanya sassaken kanyar da ganyen sabarar su bushe sai a daka su, su zama gari. Sai ana kwabawa da zuma ana shafawa a dubura lokacin da za a kwanta bacci.

Dan uwa wallahi, basir ko na gado ne da ikon ALLAH ka rabu da shi kenan har a bada.

Wannan maganin duk Wanda ya jarraba shi, in Sha Allahu sai yayi Mana, addu’ar fatan alkhairi in dai akan matsalar basir mai tsiro ne dan uwa, kawai ka jarraba kanka tsaye, in Sha Allahu Yana kone basir cikin kankanin lokaci ana shafawa har garin maganin ya kare.

Karanta Wannan  Amfanin shan ruwan bagaruwa

GA WANDA YAKE BUKATAR HADADDE IRIN NAMU YAYI MAGANA IN SHA ALLAHU MUNA DA SHI A HADE, KO KUMA WATA CUTAR DA BAN BA WANNAN BA….AKWAI TAIMAKO IN SHA ALLAHU.

IZINI AYIWA ANNABI SALATI AYI SHARE DA LIKE MASU KARAMAR WAYA SUYI SALATI 100.

اللهم صلي على سيدنا محمد وعلى اله وصحبه اجمعين

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *