Monday, December 16
Shadow

Maganin ciwon gabobin jiki

Maganin ciwon gabobin jiki (arthritis) yana da yawa kuma ya danganta da irin ciwon gabon da kake fama da shi.

Akwai magunguna na likita daga Gargajiya kuma duka zamu yi maganarsu a cikin wannan rubutu.

Ga wasu daga cikin hanyoyin da za a iya bi don magance wannan ciwo:

  1. Magungunan Rage Radadi da Kuma Inflammasi na bature:
  • Ibuprofen (Advil, Motrin)
  • Naproxen (Aleve)
  • Aspirin
  • Acetaminophen (Tylenol)
  1. Magungunan Hana Yaduwar Ciwon:
  • Methotrexate
  • Sulfasalazine
  • Hydroxychloroquine
  • Biologics (e.g., Etanercept, Infliximab)
  1. Hanyoyin Gida na Gargajiya:
  • Yin amfani da ruwan zafi da na sanyi dan maganin gabobin da ke ciwo, ana iya samun ruwan dumi a yi wanka na lokaci me tsawo. Ana kuma iya samun kankara me sanyi a nade a tsumma me kyau a rika dorawa akan gabobin dake ciwon.
  • Yin motsa jiki na musamman don rage radadi da kuma inganta motsi. Motsa jikin da ake so a yi sune, tafiya, tuka keke, ko kuma yin ninkaya.
  • Kula da nauyi, motsa jiki don rage nauyi na taimakawa sosai wajan maganin ciwon gabobi sosai, hakanan ana iya rage nauyi ta hanyar kula da irin abincin da za’a rika ci.
  1. Hanyoyin Al’ada:
  • Yin amfani da man zaitun a gabobin da ke ciwo
  • Shan shayi na musamman kamar shayin citta ko Kurkur
  • Amfani da Ridi, cin ridi ko amfani da hodar ridi wadda ake yi ta hanyar dakashi ko nikashi na taimakawa sosai wajan magance matsalar ciwon gaboni, ana amfani da babban cokali 5 kullun na hodar ridi, masana sun ce yafi maganin likita amfani wajan kawar da cutar gabobi.
  1. Shan Abinci Mai Gina Jiki:
  • Abincin da ke dauke da omega-3 fatty acids kamar kifi
  • Kayan lambu masu dauke da antioxidants kamar su kabeji da karas
  • Sauran abincin da ya kamata a rika ci sun hada da Tafarnuwa,
Karanta Wannan  Nasiha akan rayuwa

Kafin ka fara amfani da wani magani ko hanya, yana da kyau ka tuntubi likita don samun shawarar da ta dace da yanayinka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *