Friday, December 27
Shadow

Maganin daina luwadi

Babban maganin daina Luwadi shine tsoron Allah.

Alhamdulillahi tunda har Allah ya karkato da zuciyarka kake neman Maganin dena luwadi, wannan babban matakin hanyar shiriyane ka dauka wanda kuma idan Allah ya yarda Allah zai taimakeka akai.

Babban Abin yi yanzu shine ka yi tuba na gaskiya da nadama ta gaske akan cewa, ba zaka sake komawa ga wannan bakar dabi’ar ba sannan ka yi addu’a sosai ta neman gafarar Allah domin Allah yana gafarta kowane zunubi matukar ba shirka bane aka mutu ana yi.

Sannan ka roki Allah ya taimakeka wajan kokarin daina wannan dabi’ar.

Hanyoyin Daina Luwadi

Allah madaukakin sarki yana cewa, “Kace yaku bayina da kuka zalunci kawunanku(ta hanyar aikata zunubai, kada ku yanke tsammani daga rahamar Allah, lallai Allah yana gafarta duka zunubai, Lallai shine me yawan Gafara da yawan Rahama. al-Zumar 39:53.

Karanta Wannan  Amfanin shan ruwan kwai

Dan haka ka tashi tsaye ka yi addu’a ka zubar da hawaye, ka kaskantar da kanka sosai da neman amincewar Allah da Gafararsa da Rahamarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *