Babban maganin daina sata shine tsoron Allah.
Sata indai ba ta cuta bace wadda ita kuma matsayinta daban, mutum zai sawa ransa kudirin dainawa ne, da kuma tuba da mayar da abinda ya sata da yin nadama akan abinda ya aikata. Idan kuma mutum bai da halin mayar da abinda ya sata ga maishi, watau ko ya kare kuma baida dukiyar da zai mayar da madadinsa, kuma bai da karfin da zai je ya nema, watau yayi aiki ya samu kudi ya biya, to sai ya tuba ga Allah.
Akwai sata ta cuta wadda a likitance ake kiranta da sunan Kleptomania.
Ita wannan sata ta cuta tana da alaka da rashin lafiyar kwakwalwa, wanda suke da ita mafi yawanci masu hali ne kuma basu da yawa a Duniya, kuma sukan saci abinda sun ma fi karfinshi ko kuma babu abinda zai amfanesu dashi.
Hakanan masana sunce ita irin wannan cutar sata ta Kleptomania tafi yawa a tsakanin mata inda ba’a cika samun namiji da cutar ba.
Misalin me cutar sata ta Kleptomania shine mutum ne me dumbin dukiya amma sai ya saci cokali, ko biro ko tabarma da dai sauransu.
Masana kiwon lafiya sunce ita irin wannan cuta bata da magani. Sannan kuma ana gadonta.
Saidai duk wanda zai dauki abu dan amfanin kansa watau ya sayar ya samu kudi, misali mutum ya saci kudi, ko ya saci mota, ko ya saci waya, dadai sauransu, wannan sata ce ta dabi’a, maganinta, kamar yanda muka bayyana a baya shine tsoron Allah.
Ka sani ko ki sani cewa ita sata Allah yayi Allah wadai da ita sannan ya bayyana hukuncin yanke hannun dama ga duk wanda aka kama ya aikatata.
Allah madaukakin Sarki na cewa “Game da maza da mata barayi, A yanke hannunsu(watau hannun dama) a matsayin hukunci kan abinda suka aikata.(wannan) Hukuncine ta hanyar Misali daga Allah. Allah shine mafi karfi kuma mafi sani. al-Maa’idah 5:38.
Hakanan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yace, A yanke hannun akan satar data kai daya bisa hudu na zinari ko fiye da hakan. al-Bukhaari, al-Hudood, 6291.
Hakanan kuma Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya tsinewa barawo saboda yace gurbataccene a cikin Al’umma. Kuma idan ba’a hukuntashi ba, Muguwar halayyarsa zata watsu a tsakanin mutane ta gurbatasu. Annabi Muhammad(Sallallahu Alaihi Wasallam) yace, Allah ya tsinewa barawo wanda ya saci kwai aka yanke masa hannu, ko ya saci igiya aka yanke masa hannu. al-Bukhaari, al-Hudood.
Dan haka mutum ya duba girman zunubin da kuma irin hukuncin da aka tanadar masa ya gujeshi.