Thursday, January 16
Shadow

Maganin rashin sha’awa ga maza

Rashin sha’awa ga maza, matsalace da maza da yawa kan yi korafi akanta, a wannan rubutun, zamu yi bayani yanda matsalar take da abubuwan dake kawota da kuma maganinta.

Abubuwan dake kawo rashin sha’awa ga maza

Rashin Kwanciyar Hankali: Masana kiwon lafiya musamman na bangaren jima’i sun bayyana cewa, rashin kwanciyar hankali na daya daga cikin abubuwan dake kawarwa namiji sha’awa, misali a yayin da mutum ke cikin tsananin bashi kuma me kudin na nemanka ruwa a jallo, ko kuma an kori mutum daga aiki kuma bashi da hanyar ciyar da iyalansa, da dai sauransu.

Kibar da ta wuce misali: Yawan kiba na daya daga cikin abubuwan da masana kiwon lafiya sukace take rage karfin sha’awa. Musamman idan mutum ya zamana me yawan ciye-ciyene barkatai.

Karanta Wannan  Maganin rashin sha'awa ga mace

Rashin Cin Abinci me kyau: Rashin Cin abinci me kyau da kara lafiyar jiki, misali irinsu wake, madara, kayan marmari, irin su ayaba, kwakwa, dabino, yegot, tuffa, da ganye irin su alayyahu, kabeji da sauransu na iya kawo raguwar karfin sha’awa.

Rashin Motsa Jiki: Zama ba motsa jiki na taimakawa wajan rage sha’awa, hakanan ma yawan wahala ko motsa jiki da ya wuce kima shima yana kawo raguwar sha’awa Dan haka bai kamata a rika zama ba motsa jiki kwata-kwata ba, hakanan bai kamata a rika wahala da yawaba ko motsa jiki da ya wuce kima ba.

Rashin samun isashshen bacci: Hakanan rashin samun Hutu da ya kamata ko ishshen bacci yana iya rage karfin sha’awa.

Karanta Wannan  Ya ake gane mace 'yar iska

Dan haka masana kiwon lafiya sun bayar da shawarar cin abinci me kyau da motsa jiki da samun Hutu yanda ya kamata ga namijin dake fama da rashin sha’awa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *