Akwai magungunan tari na gargajiya da yawa. A wannan rubutun, zamu bayyana su daya bayan daya:
Ana hada maganin tari na gargajiya da Karas, Lemun Tsami, Suga da Zuma.
Yanda ake hadawa shine, a samu karas din a wanke sannan a daddatsashi.
A matse ruwan lemun tsamin a zubasu a mazubi daya da zuma da sukarin.
A barshi ya kai awa 24 a ajiye.
Sannan a fara sha karamin cokali kullun sau biyu a rana.
Ana kuma iya hada maganin Mura da Zuma da Albasa.
Ana yanka Albasar a saka cikin kwano, daga nan kuma sai a zuba zuma a saman Albasar.
A rufe a barshi yayi akalla awanni 12.
Bayan nan sai a fara sha.
Saidai yaro dan shekaru 2 baya sha, sannan me ciwon sugar kada ya rika sha da yawa.