Thursday, January 30
Shadow

Maganin yawan fitsari

Yawan fitsari matsala ce dake sa mutum ya rika yin fitsari fiye da kima, idan ya zamana mutum na yin fitsari fiye da sau 8 a rana, za’a iya cewa yana yawan fitsari.

Wannan matsala zata iya faruwa ga kowa amma tafi yawa a tsakanin mutanen da suka zarta shekaru 70 a Duniya, da mata masu ciki, ko bayan fara shan wani magani, ko kuma wani me wata cuta ta musamman.

Yawan Fitsari na iya zama alamar daukar ciki ga mace, sannan yana iya zama alamar ciwon sugar wanda ake cewa diabetes ko ciwon mafitsara, da sauransu.

Masana kiwon lafiya sunce ba matsala bace idan mutum ya tashi da dare yayi fitsari, sun ce idan mutum ya kai shekaru 40 zuwa 50, to zai iya fuskantar tashi cikin dare yayi fitsari sau daya. Idan kuma mutum yana tsamanin shekaru 60 zuwa 70, zai iya rika tashi cikin dare yana yin fitsari sau 2. Yawan fitsarin mutum zai iya karuwa zuwa sau 3 ko sama da haka idan ya kai shekaru 80.

Karanta Wannan  Amfanin ganyen magarya

Saidai idan yawan fitsarin yayi yawa da dare yana iya hanaka yin bacci. Matsalolin dake kawo yawan fitsari da dare sun hada da ciwon zuciya, kumburin kafafu, da matsalar rashin bacci.

Idan ya zamana kana yawan yin fitsari duk bayan mintuna 30, to lallai ya kamata ka ga likita saidai idan kana yawan shan ruwane to wannan daban.

Idan dai ya zamana yawan fitsarin da kake ya dameka kuma yana hanaka sakewa da rana ko ya hanaka bacci da dare, ya kamata a nemi Likita.

Ga hanyar maganin yawan fitsari a Gida:

A daina shan abu me ruwa awanni 2 kamin a je Kwanciya.

A daina shan giya da rage yawan shan Coffee.

Karanta Wannan  Amfanin tafasa

Allah ya Sauwake.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *