Yawan fushi matsala ce wadda idan mutum na da ita, zai yi fama da ma’amala da mutane.
A wannan rubutu, zamu yi bayani dalla-dalla kan maganin yawan fushi dan kaucewa aikin dana sani.
Idan kana da yawan Fushi, kada ka zama me yawan magana. Musamman a yayin da ranka ya baci, idan kace zaka yi magana, zaka yi dana sani akan abinda ka fada. Ka yi tunani, ko ka bari ka huce kamin kace wani abu, shima wanda ya maka ba daidai ba, ka barshi ya dawo hayyacinsa tukunna.
Masana kiwon Lafiya sun bayyana cewa, idan ka yi fushi sosai, kuma ka kasa shawo kanka, to ka je ka motsa jiki, kamar tafiya da sauri ko yin gudu.
Idan zai yiyu, ka samu guri kai kadai ka zauna ka nutsu na dan mintuna.
Idan kai musulmi ne ka yawaita ziki, da karatun Qur’ani, zaka samu saukin lamarin.
Hakanan idan a tsaye kake ka zauna, idan a zaune kake, ka kishingida, sannan ka samu ruwa ka sha.
Hakanan idan kana da kudi, ka je ka sayi abinda kafi so ka ci, kamar kaza, ice cream, burger, tsire da sauransu.
Idan kana da mata, ka je ku zauna ku yi hira ta soyayya.
Idan wani abune ya bata maka rai, ka samu wani amininka, ka bashi labari tare da neman shawararsa.
A karshe ka fawwalawa Allah komai.