Yawan mantuwa matsalace da kan saka mutum cikin damuwa musamman a ma’amalarsa da mutane da wajan aiki da sauransu.
A wannan rubutu zamu yi bayani game da yawan mantuwa da yanda ake maganinsa.
Abubuwan dake kawo yawan mantuwa:
Yawan Shekaru: A yayin da tsufa ya fara kama mutum, zai iya yin fama da yawan mantuwa saboda kwakwalwarsa bata aiki kamar lokacin da yake da kuruciya ko sauran karfi a jikinsa.
Damuwa: Wanda ke cikin yawan damuwa kan samu matsalar mantuwa musamman idan damuwar ta yi yawa.
Rashin Isashshen Bacci: Wanda baya samun bacci ko rashin isashshen bacci kan iya yin fama da matsalar yawan mantuwa.
Rashin Cin Abinci me gina Jiki: Rashin cin Abinci me gina jiki na iya taba lafiyar kwakwalwar mutum wanda ke iya kaiwa ga yawan mantuwa. Hakanan yawan shan sikari da rashin shan wadataccen ruwa duk zasu kaiwa ga matsalar mantuwa
Matsalolin kai, irin su ciwon kai me tsanani ko wasu kalar magungunan da mutum ke sha na iya kaiwa ga har ya samu matsalar kwakwalwa da zata iya kaishi ga cutar mantuwa.
Yanda Ake Maganin yawan mantuwa:
Motsa Jiki: Ga wanda ke fama da mantuwa, motsa jiki na da matukar Amfani dan kuwa zai sa kwakwalwar mutum ta rika aiki yanda ya kamata. Ko da kuwa tafiyace da sauri ta minti talatin a kowace rana ta wadatar.
Samun Wadataccen Bacci: Ya kamata a rika samun wadataccen bacci, idan mutum ya kwanta bacci, kwakwalwarsa ma na hutawa sannan ta dawo aiki da karfi yanda ya kamata idan ya tashi daga baccin.
A rage saka kai Damuwa: Mutum ya rika kokarin gujewa duk wani lamarin da zai saka rayuwarsa cikin damuwa. Ya rika kaucewa fada, gaddama, da sauransu.
A rika yin wani abu da zai sa Kwakwalwa tunani: Mutum ya rika yin karatun littafi, ko kuma wani dan wasa da zai sa kwakwalwarsa yin tunani.
A rika kuma yin kokari ana haduwa da abokai da ‘yan uwa ana tattauna lamuran rayuwa da shawarwari da sauransu.
Me fama da matsalar yawan mantuwa ya kamata ya rika cin abinci irin su kifi, ganyayyaki irin su alayyahu, Kabeji, da sauransu, ya kuma rika amfani da man zaitun, da cin Alkama.
Sannan mutum ya rage yawan ci da shan abubuwan Kwalba dana leda dana roba wanda kamfanoni daban-daban ke yi.
Allah ya sauwake.