
Kwamishinan ‘yansanda na jihar Delta, CP Olufemi Abaniwonda ya tabbatar da cewa wani mutum me suna Paul ya cakawa kaninsa wuka ya mutu har lahira saboda ya mari matarsa.
Lamarin ya farune a Ugbokodo, dake karamar hukumar Okpe.
Shima kakakin ‘yansandan jihar, SP Bright Edafe ya tabbatar da faruwar lamarin.
Yace kudin matar yayan nasa ne suka bace Naira Dubu biyu wanda ta zargeshi da dauka shi kuma yace bashi ya dauka ba.
Saidai ita ta nace cewa shi ya dauka inda har ta cukumeshi anan ne mahawara ta yi zafi inda ya falla mata mari.
Nan ta tafi ta kira mijinta ta gaya masa, shi kuma ba tare da bincike ba ya dauki daya daga cikin ‘ya’yansa suka bi kanin nasa suka dakeshi da caka masa wuka har ya mutu.
Jama’ar unguwar sun kona gidan mutumin da shagon matarsa inda saida ‘yansanda da sojoji suka kai dauki sannan hankula suka kwanta.
Tuni dai aka kama wanda ake zargi.