Saturday, January 11
Shadow

Mahaukaciyar gobara da ba’a taba ganin irin taba ta babbake gidaje dubu goma a birnin Los Angeles na kasar Amurka, mutane 11 sun mùtù

Wutar daji a birnin Los Angeles na kasar Amurka ta yi sanadiyyar mutuwar mutane 11.

Hukumomin lafiya na birnin Los Angeles sun ce 5 daga cikin anda suka mutu sun mutu ne a yankin Palisades sai kuma guda 6 sun mutu ne a yankin Eaton.

Har yanzu dai mahukunta basu san dalilin tashin wannan gobara ba.

Hakanan an samu karancin ruwan kashe gobarar kuma ma’aikatan kashe gobarar ma sun yi karanci inda makwauciyar kasar Amurka, Mexico ta aike da taimakon masu kashe gobara zuwa birnin na Los Angeles.

Ana dai zargin mahukuntan birnin na Los Angeles, Musamman Gwamnan California, Gavin Newsom da Magajiyar garin da sakaci wajan rashin yin tanadin yanayi irin wannan inda ake zargin basu dauki matakin adana ruwan sama da aka samu me yawa ba dan kashe gobara irin wannan ba.

Karanta Wannan  Hoto: An kama wani mutum da muggan makamai a Abuja

Hakanan an zargi hukumomin da rage kudin kar ta kwana na yaki da gobarar daji a cikin kasafin kudin da suka yi.

Gobarar tatilasta kulle makarantu da kasuwanni a birnin.

Hakanan a ranar Juma’a, mahukuntan birnin sun sanar da cewa gidaje sama da dubu goma ne gobarar ta lalata sannan ana kan kokarin tseratar da mutane dubu dari da hamsin daga gobarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *