Friday, May 23
Shadow

Majalisa ta yi watsi da ƙudirin karɓa-karɓan shugabanci a Najeriya

Majalisar wakilai ta yi watsi da wani ƙudirin doka mai neman tabbatar da tsarin karɓa-karɓan shugabanci a Najeriya.

Wannan na daga cikin aikin da majalisar ke yi na gyaran wasu sassa shida na kundin mulkin ƙasar, waɗanda a baya suka gaza tsallake karatu na biyu a zauren majalisar.

Zaman majalisar na ranar Talata wanda shugabanta Abbas Tajudeen ya jagoranta ya yi muhawara a kan ƙudirin sannan ya cimma matsayar yin watsi dashi kamar yadda ya yi wa sauran ƙudirorin da aka gabatar da su tare.

Sai dai ana sa ran batun zai ƙara tasowa a zaman majalisar wakilan na yau Laraba domin sake tafka muhawa da ɗaukar matsaya a kai.

Karanta Wannan  Tinubu ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2025

Wasu daga cikin ƴan majalisar da suka yi muhawara a kan ƙudirin sun ce a yanzu haka jam’iyyun siyasar Najeriya suna da irin nasu tanadi na tantance karɓa-karɓan shugabanci a Najeriya, kuma akwai hukumar tabbatar da daidaito, wadda ke aikin da ake neman ƙudirin ya yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *