
Majalisar dattijai ta ce bata da masaniya game da zargin da sanata Natasha Akpoti kewa kakakin majalisar, Sanata Godswill Akpabio na neman yin lalata da ita.
Me magana da yawun majalisar, Senator Adeyemi Adaramodu ne ya bayyana haka a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV inda yace Sanata Natasha Akpoti bata gabatar wada kwamitin ladabtarwa na majalisar zarge-zargen da takewa Sanata Godswill Akpabio ba.
Yace dan haka ba ruwansu da maganar ba zasu dauki mataki akan abinda ke faruwa a kafafen sadarwa na yanar gizo ba ko kuma gidajen watsa labarai ba.