
Majalisar wakilai na son a maida yin zaɓe ya zama wajibi ga ƴan Nijeriya
Wani ƙudiri da ke neman maida yin zaɓe ya zama wajibi ga ƴan Nijeriya ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai.
Ƙudurin, wanda shugaban majalisar, Tajuddeen Abbas ya ɗauki nauyi, ya tsallake karatu na biyu bayan an yi wata zazzafar muhawara a zauren majalisar a yau Alhamis.