
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya nemi yin taro da kasashen Duniya wanda suka hada da China, da Rasha inda yace zai bayar da shawarar su taru su 3 din suk su rage yawan makaman da suke dasu.
Shugaban yace maimakon kashe makudan kudaden da suke akan tsaro, kamata yayi su mayar da hankali wajan kashe irin wadanna kudaden akan ayyukan ci gaban wa mutanen kasarsu.
Yace zai nemi duka su ukun su rage kashe kudi akan tsaro da kaso 50 cikin 100 watau su raba kudin gida biyu inda yace yayi amannar kuma zasu amince.
Trump yace a yanzu Amurka na da makamai na kare dangi wanda zasu iya lalata Duniya har sau 100 dan haka babu bukatar a ci gaba da kera makaman kare dangi.
Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da shugaban India, Nedradi Modi.