
Mahaifiyar shahararren mawakin Najeriya, 2face Idibia, Rose Idibia ta roki cewa a yi magana da sabuwar Budurwar dan nata ‘yar majalisar jihar Edo, Natasha ta kyale danta.
Rose ta bayyana hakane a wani faifan bidiyon da ta saki.
Tace dan nata yana kokarin sakin matarsa, Annie amma dai tasan cewa, baya cikin hayyacinsa, tacewa Natasha ta cire sakar data ratayawa dan nata dan ya dawo hayyacinsa.
2face Idibia dai ya rabu da matarsa, Annie inda ya koma soyayya da sabuwar budurwarsa,Natasha kuma yace ita zai aura.