Monday, December 16
Shadow

Masoya Aminu Ado Bayero sun yi Sallar Rokon Allah ya dawo dashi kan sarautar Kano

Masoya tsohon sarkin Kano, Aminu Ado Bayero sun yi Sallah inda suka roki Allah ya dawo dashi kan sarautar Kano.

Ranar Alhamis ne dai majalisar Kano ta soke dokar data kirkiro masarautu 4 a Kano sannan ta sauke Aminu Ado Bayero inda aka dawo da tsohon Sarki, Muhammad Sanusi II kan karagar Sarautar.

Saidai Aminu Ado ya koma Kano inda ya je gidan Nasarawa ya kafa fadarsa acan, kuma masoyansa sun mai maraba.

An ga masoyan Tsohon sarkin da yawa suna Sallah inda suke rokon Allah ya dawo dashi kan karagar sarautar Kano.

Karanta Wannan  Kungiyar Kwadago zata tafi yajin aikin sai mama ta gani saboda gazawar Gwamnati na aiwatar da mafi karancin Albashin dubu 70

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *