
Babban Malamin addinin Islama Sheikh Yusuf Guruntum ya jawo hankalin masu laifi musamman Mazinata da su tuba kamin lokaci ya kure musu.
Malam ya bayyana hakane a wajan wa’azin da yake na watan Ramadana inda yace idan ka yi laifi to zaga ka ba daidai ba saidai fa idan ka Tuba.
Malam ya bayar da misali da mazinata yace su tuba su daina, idan ba haka ba kuwa suka bari lokaci ya kure musu, zasu hadu da fushin Allah.