Hukumar hana yaɗuwar cututtuka ta Najeriya NCDC ta fitar da sanarwar fadakar da jama’a game da ƙaruwar kamuwa da cutar kwalara a fadin kasar yayin da damina ke ƙara kamari.
An samu rahoton bullar cutar a jihar Legas a baya-bayan nan, lamarin da ya ƙara dagula al’amura.
Daga ranar 1 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Yunin 2024, an samu jimillar mutum 1,141 da ake zargi da kamuwa da cutar kwalara da kuma 65 da aka tabbatar sun kamu da cutar, kuma mutum 30 sun ne suka mutu duk daga ƙananan hukumomi 96 a faɗin jihohi 30 sakamakon cutar.
Jihohin da suka fi fama da cutar, waɗanda ke bayar da kashi 90% na yaɗuwar cutar sun hada da Bayelsa da Zamfara da Abia da Cross River da Bauchi da Delta da Katsina da Imo da Nasarawa da kuma Legas.
Kungiyar kwararru kan hana yaɗuwar cuttutuka ta kasa da dama, karkashin jagorancin NCDC da suka hada da ma’aikatun muhalli da albarkatun ruwa na tarayya da Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko ta kasa (NPHCDA) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF). ) da sauran abokan hulda, sun kasance suna tallafawa jihohin da abin ya shafa.
Wannan tallafin ya haɗa da bayar da bayyanai kan haɗarin kamuwa da cutar da bincike mai aiki da ɗorewa, da binciken ɗakin gwaje-gwaje, da yaɗa bayanai na wayar da kan jama’a kan cutar kwalara a cikin Ingilishi da harsunan gida da dai sauransu.