Friday, December 5
Shadow

Masu Laifi 16 sun tsere daga gidan gyara hali dake Keffi jihar Nasarawa

Masu laifi 16 ne suka tsere daga gidan gyara hali na Keffi dake jihar Nasarawa

Lamarin ya farune da sassafiyar ranar Talata.

Me magana da yawun hukumar kula da gidajen gyara hali na kasa, Umar Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace jami’an hukumar 5 ne suka jikkata sanadiyyar lamarin.

Yace 2 daga ciki suna cikin mawuyacin hali

Saidai yace an kama 7 daga cikin wadanda suka tsere kuma ana bin sahun sauran.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna: Mun cinye zaben shekarar 2027 mun gama>>Inji Ganduje Bayan da ya karbi 'yan NNPP da suka koma APC

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *