
Wata Kungiyar matan yarbawa a jihar Osun ta yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Alkawarin kuri’u Miliyan 1 a zaben 2027.
Kungiyar tace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne zabinta a zaben 2027.
Matan ta bakin wakiliyarsu a jihar Osun, Adesola Ayangbil sun bayyana cewa, sun fara yakin neman zabe ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu gida’gida kamin zuwa zaben shekarar 2027.
Sun bayyana hakane a ofishin yakin neman zaben Tinubu da Shettima.
Sun ce sun yaba da shugabancin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekaru 2 da suka gabata.