Saturday, November 8
Shadow

Matan Yarbawa sun yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Alkawarin samar masa da kuri’u Miliyan 1

Wata Kungiyar matan yarbawa a jihar Osun ta yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu Alkawarin kuri’u Miliyan 1 a zaben 2027.

Kungiyar tace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne zabinta a zaben 2027.

Matan ta bakin wakiliyarsu a jihar Osun, Adesola Ayangbil sun bayyana cewa, sun fara yakin neman zabe ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu gida’gida kamin zuwa zaben shekarar 2027.

Sun bayyana hakane a ofishin yakin neman zaben Tinubu da Shettima.

Sun ce sun yaba da shugabancin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekaru 2 da suka gabata.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Motarnan tawa da kuke gani, zata sayi motar Rarara guda 3 hadda canji, in baku yadda ba, ku tambayi Sarkin Mota>>Inji Naziru Sarkin Waka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *