
Matar da tafi kowace mace kudi a Najeriya da Afrika, Folorunso Alakija ta makance kwata-kwata inda ta daina gani gaba daya.
Rahoton hakan ya fito ne daga kafar Sahara Reporters inda suka ce ta samu wannan matsalane dalilin hawan jini.
Lamarin ya farane a yayin da suke tafiya tare da mijinta a cikin jirgi inda jirgin ya so samun tangarda.
Daga nan ne dai sai ta fara ganin hazo-hazo, wasu na kusa da ita sun bayyana cewa bata dauki wani matakin neman magani da muhimmanci ba kan lamarin wanda hakanne yasa ta kai ga makancewa gaba daya.