Thursday, October 3
Shadow

Matar soja Abbas mai suna Husaina Iliyasu ta cika gwarzuwa kuma jarumar da samun irin ta sai an tara mata 1000

TSANTSAR RASHIƝ IMÁNI DA TAÚSÁYI

Matar soja Abbas mai suna Husaina Iliyasu ta cika gwarzuwa kuma jarumar da samun irin ta sai an tara mata 1000.

Mijinta soja ne Mųsưlmi wanda daga zuwa yin Sálląh yayin da ake bakin aiki shine ogansa ya sa shi a gaba shekara da shekaru a garƙame sai da ya haukatar da shi.

Tsantsar tsagwaron rashin imani ya ƙare a wannan labarin. Shin ina manyan Musulmi dake aikin soja a ƙasar nan? Shin wa ya ce a keta alfarmar ɗan adam saboda bambancin addini a aikin soja?

Ina kungiyoyin kare hakkin mata? Ina kungiyar kare hakkin dan Adam? Ina kungiyar manyan Arewa? Ina kungiyar lauyoyi Musulmi? Ina kungiyar Malaman mu? Ina kungiyar yan jaridun kasar nan?

Karanta Wannan  Tsohon Ministan Sadarwa Da Tattalin Arzikin Zamani Farfesa Isa Ali Pantami Ya Ziyarci Hajiya Turai Umaru Musa Yar'adua Domin Yin Ta'aziyyar Rasuwar Mahaifiyar Tsohon Shugaban Kasa, Hajia Dada A Gidanta Dake Abuja

Mutun ya sadaukar da rayuwar sa don ya kare ƙasa amma a ƙarshe saboda son zuciyar wani a mayar da shi mahaikaci kuma dabba ta karfi da yaji.

Ya kamata a hukunta masu hannu a wannan babban laifi mafi muni da bai kamata ya faru a wannan lokaci ba.

Daga Maje El-Hajeej Hotora

DA ƊUMI-ƊUMI: Bayanai daga majiya mai tushe suna nuna cewa yanzu haka maganar Hussaina da mijinta Abbas ta je gaban manya kuma za ayi bincike dan tabbatar da abinda matar ta faɗa kuma ana sa rai shi wancan mutum MS Adamu da ta ambata sai ya girbi abinda ya shuka

Malam Yasir Ramadan Gwale ya yi ƙarin hasken cewa “Babu shakka labarin Hussaina da mijinta Abbas akwai tashin hankali da damuwa kwarai da gaske. Abu mai daɗi shi ne yanzu haka maganar ta je gaba kuma zai ai bincike dan tabbatar da abinda matar ta faɗa. In sha Allah, shi wancan mutum Adamu sai ya girbi abinda ya shuka da yardar Allah. Allah ka kiyayemu fitinar rayuwa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda aka tursasawa matashi ya karbi dansa bayan da yawa budurwarsa cikin shege

Ya ‘yan uwa mu dage da adduoin irin waɗan da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya koyar musamman na fitinar rayuwa da mutuwa. Allah ka tsare mu a yayin da muke Raye ka kare mu ka rufa mana asiri har bayan mutuwarmu”.

Menene fatan ku?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *