
Me martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyanawa matasa cewa cikin sauki zasu karbe mulki a kasarnan indai suka ce abinda ake musu ya isa haka.
Ya bayyana hakane a wajan wani taron marubuta da aka yi, kamar yanda gidan talabijin na Channels TV ya ruwaito.
Sarki Sanusi yace Najeriya ta yi fama da rashin shuwagabanni na gari wanda hakan ya hanata samun ci gaban da ya kamata.