
Shugaban tsohuwar kungiyar goyon bayan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Dr. Jibril Mustapha, ya yi kiran tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya fito takarar shugaban kasa a shekarar 2027.
A sanarwar da ya fitar a Legas, yace ya kamata tsohon shugaban kasar ya amsa kiraye-kirayen da ake masa domin shine Najeriya ke bukata a yanzu.
Yace Najeriya a yanzu tana bukatar shugaban kasa wanda zai hada kan kasar kuma Tsohon shugaba Goodluck Jonathan na da wannan abun da ake bukata.