
Wata Kungiya me sun, Agramondis Research and Consulting ta bayyana cewa matsalar Tsaro ta jawowa Najeriya asarar Naira Tiriliyan 7.17 sannan kaso 40 cikin 100 na dabbobin da ake dasu sun salwanta.
Rahoton yace bangaren dabbobi na taimakawa da kaso 10 cikin 100 na ci gaban Najeriya sannan ya samarwa mutane Miliyan 4.5 aikin yi amma gwamnati bata zuba jari sosai a bangaren.
Kungiyar tace fari, Canjin Yanayi da matsalar tsaro, da karancin ruwan sama da rikicin manoma da makiyaya na kawowa bangaren tsaikon ci gaba.
Dan hakane ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta kawo dauki a hangaren ta hanyar ilimantar da manoma da makiyaya da basu tallafi da kayan aiki na zamani