
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya bayyana cewa matsalar tsaron Najeriya bata yi munin da za’a fara cewa ‘yan Najeriya su tashi su kare kansu ba.
A hirar da aka yi dashi a Channels TV yace karfafa mutane su rika kare kansu daga harin ‘yan Bindiga zai kai ga kara munana lamarin.
Ya bayyana hakane biyi bayan maganar tsohon Ministan tsaro, T.Y Danjuma da yace mutane su rika tashi tsaye suna kare kansu daga masu kai musu hare-hare inda yace gwamnati ka dai ba zata iya ba
Saidai Gwamna Umar Namadi yace Danjuma mutum ne wanda bai da wasa amma shi a nashi ganin Gwamnatin tarayya tana kokari duk da yake cewa ba duka matsalar take iya magancewa ba amma tana iya bakin kokarinta.
Yace a kokarin magance matsalar rikicin makiyaya da manoma, yayi amfani da Sulhu wanda yace kuma an samu Nasara.
Dan haka yace yana ganin bin hanyar sulhu zai fi dacewa.