Ga abinda ake karantawa a Sallar Gawa kamar haka:
Bayan kabbarar farko ana karanta Fatiha.
Bayan Kabbara ta biyu ana karanta Salatin Annabi(SAW).
Bayan kabbara ta uku sai a yiwa mamaci addu’a.
Bayan kabbara ta hudu sai mutum yawa kansa addu’a.
Shikenan kuma sallama daya ake yi.