Naso na nufin likewar wani abu a jikin wani abu ko kuma bayyanar wani abu a jikin wani abu dalilin haduwarsa da wani Abu.
Misali, idan ka zuba ruwan sanyi a cikin kofi, zai yi naso a jikin kofin ta baya inda zaka rika ganin kamar zufa a bayan kofin.
Ko kuma idan ka samu rigar bakanike, zaka ga bakin mai ya manne a jikinta, wannan mannewar ita ake kira da Naso.
Ko kuma idan gini yana kusa da ruwa, zaka ga kasan katangar ginin kamar ta jike, wannan ma naso ne.
Ina fatan wadannan misalai dana baka sun sa ka fahimci ko kin fahimci me ake nufi da Naso a Hausa.