Hukumar ‘yansandan Najeriya ta kama wani jami’inta a South Ibie dake jihar Edo saboda zargin yawa karamar yarinya me shekaru 16 fyade a ofishin ‘yansandan.
Wata ‘yarsanda mace ta dauki bidiyon faruwar lamarin inda aka ga dansandan na saka wando bayan an kamashi.
Ya samu damar yiwa yarinyar fyadene bayan da ta fita hayyacinta.
Kakakin ‘yansanda na kasa, ACP Olumuyiwa Adejobi ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace an gano dansandan da yayi wannan aika-aika kuma ana bincike akansa.
Ya bayyana sunan dansanda da Sergeant Abraham Uzuobor inda yace sun yi Allah wadai da abinda ya aikata.
Yarinyar dai an kamata ne bisa zargin aikata wani laifi inda aka barta da Sergeant Abraham Uzuobor ya binciketa amma ya buge da yin lalata da ita.