Saturday, August 8
Shadow

Me sayar da kosai akan Naira dubu ashirin da biyu

Wata mata ta bayyana a Legas dake sayar da kosanta akan Naira 22,000.

Matar dai a Lekki take kuma sunan wajan sayar da kosan nata The Akara Lekki.

Lamarinta ya dauki hankula a kafafen sada zumunta saboda an saba sayen Kosai akan Naira 50 zuwa 100 amma nata ya zo da farashi me tsada.

A kariyar data rika baiwa kanta, matar tace, kosanta ba irin na sauran bane, ba kosai bane kawai, takan saka kifi, Nama hadda ma kaza a ciki.

Sannan wajanta akwai tsafta, hakanan unguwar da take Lekki babbar unguwa ce wadda kama shago na da tsada.

Karanta Wannan  Kalli Karin Hotuna da Bidiyo daga faduwar da jirgin kasan dake jigila tsakanin kaduna zuwa Abuja yayi a yau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *