Monday, December 16
Shadow

Me zai faru da shari’o’in da ake yi wa Trump bayan ya lashe zaɓe?

Bayan shafe makonni ana gwagwarmaya a yaƙin neman zaɓe, an ayyana Donald Trump na jam’iyyar Republican a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar Amurka.

Tsohon shugaban ƙasar, shi ne na farko da aka samu da laifi, kuma zai kasance na farko da zai fara aiki yayin da ake ci gaba da sauraron shari’o’in laifuka da dama a kansa.

Shigarsa ofishi mafi girma a Amurka yayin da yake fuskantar tuhume-tuhume da dama ya jefa ƙasar cikin wani lamarin da ba a taɓa ganin irinsa ba.

Ga abin da zai iya faruwa da ƙalubalen shari’a guda huɗu da yake fuskanta yayinda ya ke shirin komawa Fadar White House.

Samunsa da laifin biyan kuɗin toshiyar baki a New York

Tuni aka yanke wa Donald Trump hukunci kan laifuka 34 da suka haɗa da shirga karya kan bayanan kasuwanci a jihar New York.

A watan Mayu, wani alƙali a New York ya same shi da laifukan da ake tuhumarsa da suka danganci biyan kuɗaɗen toshiyar baki ga wata tauraruwar fina-finan batsa.

Alƙalin New York Juan Merchan ya jinkirta yanke hukunci kan Trump daga watan Satumba zuwa ranar 26 ga Nuwamba, bayan zaɓe.

Mai shari’a Merchan na iya yanke hukuncin kamar yadda aka tsara duk da nasarar da Trump ya samu, in ji tsohuwar mai gabatar da ƙara a Brooklyn Julie Rendelman.

Karanta Wannan  Gwamnin ban tausai:Ji yanda mutane suka nutse a ruwa yayin da suka shiga kwale-kwale dan tserewa harin 'yan Bin-di-ga a jihar Naina

Masana harkokin shari’a sun ce da wuya a yanke wa Trump hukuncin ɗauri a gidan yari sakamakon cewa wannan ne karon farko da ake samunsa da laifi.

Amma idan har aka yi masa haka, lauyoyinsa za su ɗaukaka ƙara kan hukuncin cikin gaggawa, suna masu cewa zaman gidan yari zai hana shi gudanar da aikinsa na hukuma, kuma ba za a tsare shi a lokacin da ya ke ɗaukaka ƙaran ba, in ji Ms Rendelman.

“Ana iya kwashe shekaru ana ɗaukaka ƙara a cikin wannan yanayin,” in ji ta.

Shari’ar kutsen ranar 6 ga watan Janairu

Mai shigar da ƙara na musamman Jack Smith ya shigar da ƙara kan Trump a shekarar da ta gabata kan yunƙurinsa na juya kayen da ya sha a zaɓen 2020 a hannun Joe Biden.

Trump dai ya musanta aikata ba daidai ba.

Shari’ar ta kasance cikin ruɗani tun lokacin da kotun ƙoli ta yanke hukunci a wannan bazarar cewa Trump na da kariya a wani ɓangare daga tuhumar aikata laifuka kan ayyukan hukuma da ya aikata yayin da yake kan karagar mulki.

Tuni dai Smith ya sake sabunta kararsa, yana mai cewa yunƙurin Trump na juya sakamakon zaɓen ba shi da alaƙa da aikinsa na shugaban ƙasa.

Tun da Trump ya yi nasara, yanzu matsalolinsa na shari’a za su watse, a cewar tsohon mai gabatar da ƙara na tarayya Neama Rahmani.

Karanta Wannan  Hedikwatar Tsaro Ta Kasa Ta Yi Wa Babban Soja MS Adamu Gayyatar Gaggawa Domin Ya Zo Ya Yi Bayanin Dalilinsa Na Azabtar Da Soja Abbas Har Na Tsawon Shekaru Shida

“An tabbatar da cewa ba za a iya gurfanar da shugaban ƙasa mai ci ba, don haka za a yi watsi da shari’ar magudin zaɓen a kotun gundumar DC,” in ji shi.

Mista Rahmani ya ce, idan Smith ya ki yin watsi da ƙarar, Trump na iya kawar da shi kawai, kamar yadda ya yi alƙawarin yin hakan.

“Zan kore shi a cikin daƙiƙa biyu,” in ji Trump yayin wata hirar gidan rediyo a watan Oktoba.

Shari’ar takardun sirri

Har wa yau, Smith yana jagorantar shari’ar da ake yi wa Trump kan zargin karkatar da wasu takardu na sirri bayan ya bar fadar White House, zargin da Trump ya musanta.

Ana zarginsa da adana wasu muhimman takardu a gidansa na Mar-a-Lago da kuma kawo cikas ga kokarin da ma’aikatar shari’a ta yi na kwato taƙardun.

Alƙalin da ke sauraron shari’ar, wanda Trump ya naɗa Aileen Cannon, ta yi watsi da tuhumar a watan Yuli, tana mai cewa ma’aikatar shari’a ta nada Smith bisa kuskure.

Smith ya daukaka ƙara kan hukuncin.

Amma yayin da Trump zai hau karagar mulki, yanzu shari’ar bayanan sirri na fuskantar makoma iri ɗaya da na zaɓen, in ji Mista Rahmani.

Karanta Wannan  Rahotanni sun ce, Israela ta kashe Falasdinawa 50 a wani mummunan hari data kai Rafah, Kalli Bidiyon yanda mutane suka kone kurmus

“DOJ za ta janye ƙarar da ta daukaka kan shari’ar bayanan sirrin,” in ji shi.

Shari’a kan zaɓen Georgia

Haka nan, Trump na fuskantar tuhumar aikata laifuka a Georgia saboda ƙoƙarin da ya yi na juya sakamakon zaɓen 2020 a jihar.

Wannan shari’ar dai ta fuskanci matsaloli da dama, ciki har da ƙoƙarin korar lauyar yankin Fani Willis shiga saboda alaƙarta da wani lauya da ta ɗauka aiki a kan shari’ar.

Kotun daukaka ƙara tana kan nazarin ko ya dace a bar Willis ta ci gaba da kasancewa mai gabatar da ƙarar.

Amma yanzu da Trump ya zama shugaban ƙasa mai jiran gado, shari’ar na iya fuskantar ƙarin jinkiri, ko kuma ta yiwu a yi watsi da ita baki ɗaya.

Ana sa ran za a dakatar da shari’ar a lokacin da Trump ke kan karagar mulki, a cewar masana shari’a.

Lauyan Trump Steve Sadow ya faɗi haka a lokacin da alƙali ya tambaye shi ko har yanzu Trump na iya tsayawa a shari’a idan aka zabe shi.

“Amsar wannan ita ce, na yi imani cewa a ƙarƙashin dokar mulki da kuma aikinsa a matsayin shugaban Amurka, wannan shari’ar ba za wannan shar’iar ba za ta gudana ba har sai bayan wa’adinsa na mulki,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *