Akwai magunguna da yawa da ake amfani dasu dan a dade ana jima’i.
Ga wasu daga cikinsu kamar haka:
Cin Ayu, Dodon kodi da sauransu: Masana sunce cin irin wadannan kayan ruwan na taimakawa mutum ya samu karfin yin jima’i.
Shan Chakulan, ko Chocolate: Masana sun ce shan alawan Chakulan na taimakawa matuka wajan baiwa namiji kuzari.
Kankaka: Masana sun ce shan kankana yana taimakawa namiji sosai wajan samun kuzari da gamsar da iyali.
Ayaba: Masana sun tabbatar da cewa cin Ayaba yana taimakawa namiji ya samu kuzari sosai yayin kwanciya da iyali.
Cin Kifi, Musamman Sardines yana taimakawa namiji sosai wajan samun kuzarin kwanciya da iyali.
Masana sun ce domin samun dadewa ana jima’i da gamsuwa:
A daina saka kai damuwa sosai.
A daina shan giya.
A daina shan Taba.
A rika motsa jiki.
A rika amfani da kwandam.
Idan an ji za’a kawo yayin jima’i a dakata.
Idan lamarin yayi kamari a tuntubi likita.
[…] a matsayin aphrodisiac (abun da ke ƙara sha’awa) a al’adu da dama. Yana taimakawa wajen ƙara ƙarfin jima’i da kuma inganta aikin gaban […]