
Matashiya ta bayyana cewa taje coci sanye da kayan da take ganin basu da wata matsala amma Fasto ya gaya mata cewa ta yi shigar banza.

Matashiyar me suna Isabella Onyeka ta saka Bidiyon kayan a shafinta na Tiktok inda take tambayar menene matsalar kayan nata.