
Matar tsohon shugaban kasa, Dame Patient Jonathan ta bayyana cewa, Mijinta ba zai nemi takarar shugaban kasa ba.
Ta bayyana cewa, Maimakon haka, zata hada kai da matar shugaban kasa, Remi Tinubu dan su yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yakin neman zabe.
Ta bayyana hakane a yayin wata kyautar karramawa da aka bata a Abuja.
Tace a baya lokacin da mijinta ya fito takarar shugaban kasa a 2011 Itama Remi Tinubu da mijinta shugaban kasa sun taimaka musu.