Monday, December 16
Shadow

Minti nawa akeyi ana jima i

Mintunan da ake yi ana Jima’i me gamsarwa basu da yawa.

Masana sun bayyana cewa, Jima’i da aka ka yi minti daya zuwa biyu ana yi, yayi kadan sosai.

Sannan jima’in da aka yi mintu 3 zuwa bakwai ana yi, ya gamasar.

Amma an fi son a yi mintuna 7 zuwa 13 ana jima’i, shine za’a samu cikakken jin dadin jima’in.

Hakanan masana sun ce, jima’in da aka yi mintuna 10 zuwa 30 ana yi, yayi yawa, bai kamata ba, zai iya cutarwa.

Dan haka duk wadannan masu maganin gargajiyan da suke cewa wai a sha maganin su ayi awa guda ana jima’i, wannan duk salon sayar da maganine wanda kuma zai iya zama cutarwa ga namijin ko kace muddin za’a kai awa guda ana jima’i.

Karanta Wannan  Yadda ake gane mace mai ni'ima tun kafin aure

Ko da minti biyar aka yi ana jima’i ya wadatar.

Wani bincike yace yawanci mutane suna yin jima’i ne a cikin mintuna 5.4.

Saidai kuma wani binciken yace babu wani lokaci da za’a ware ace shine daidai na yin jima’i, saboda kowane mutum da irin halittarsa, wani sha’awarsa a kusa take, watau da an fara jima’i bai dadewa yake kawowa, wani kuma sha’awarsa a nesa take, sai an dade ana yi yake gamsuwa.

Wasu suna iya kai har minti 44 suna jima’i.

Babban abin da ya kamata shine ma’aurata su fahimci yanayin halittar juna da kuma yanayin karfin sha’awar junansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *