
Kungiyar Tuntuba ta Arewa me suna ACF ta bayyana cewa, abin takaici ne ya da ‘yan Arewa a kudancin Najeriya ba’a sayar musu da gidaje da Filaye.
Amma nan a Arewa ‘yan kudu na ta mallakar gidaje da filaye.
Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar, Alhaji Bashir Dalhatu ne yayi wannan kirafi inda yace ya kamata a jihohi 19 na Arewa a fito da sabon tsarin mallakar fili da gida dan magance wannan matsala.
Yace musamman a jihohin Inyamurai basa sayarwa da ‘yan Arewa fili.
Yace idan ba’a tashi tsaye aka magance wannan matsala ba, muna ji muna gani zamu sama bamu da fili ko gida a garuruwan mu duk baki sun saye.