Babban Malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa a kyale mutane su dandana wahalar Rayuwa watakila hakan zai sa su shiga taitayinsu ta yanda zasu rika kalubalantar azzaluman shuwagabanni.
Ya bayyana hakanne da yammacin yau, Juma’a, 7 ga watan Yuni yayin da yake karatun littafin Muktasar a masallacin Sultan Bello dake Kaduna.
Malam ya kara da cewa, mutane suna da wakilai a majalisar tarayya idan akwai abinda basa so zasu iya gayawa wadannan wakilai cewa shugaban kasa ya canja idan ba haka ba zasu cireshi.
Malam ya kara da cewa, hakanan mutane zasu iya yiwa dan majalisarsu Kiranye wanda baya wakiltarsu yanda ya kamata.
Malam ya kuma yi magana akan mutanen dake wulakanta kansu a wajan masu rike da mukamai cewa Allah bai saka abincin wani a hannun wani ba ta yanda sai ya wulakanta kansa sannan za’a bashi.
Wakilin hutudole.com da ya halarci karatun ya ruwaito cewa a karshe dai malam ya bayyana cewa, a daina tausayawa mutane, a barsu idan suka sha wahala watakila zasu shiga taitayinsu.