Shugaban riko na Jam’iyyar PDP, Umar Damagum ya bayyana cewa, sune suka gogar da tsohon Gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso har ya zama abinda ya zama yanzu.
Damagun ya bayyana hakane a wata ganawa da yayi da BBChausa.
Yace koda duka jam’iyyun hamayya zasu hade ba zasu yi nasarar kwace mulki daga hannun APC ba tare da PDP ba.
Kwankwaso a baya ya soki Jam’iyyar PDP inda ya bayyana irin rashin kyautawar da suka masa data sa ya fice daga cikin Jam’iyyar.
Saidai Damagun yace duk da kalubalen da Jam’iyyar ta PDP ke fuskanta amma har yanzu tana nan da kwarjininta.