
Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung da Dan takarar shugaban kasa kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore sun nemi a baiwa ‘yan Najeriya damar rike Bindiga dan su kare kansu.
Sunce idan aka yi hakan za’a daina kashe-kashen da ake yi a jihohin Benue da Filato da sauransu.
Sun bayyana hakanne a wata ganawa da suka yi da manema labarai a Abuja.
Hakan na zuwane watanni 5 bayan da Sanata Ned Nwoko ya kai kudirin neman a baiwa mutane damar rike makamai dan kare kansu.
Shima lauya dan fafutuka, Deji Adeyanju yace idan dai jami’an tsaro ba zasu iya ba, ya kamata a baiwa mutane damar sayen bindiga dan kare kansu.
Sowore yace mutane sun daina yadda da kariyar da jami’an tsaro ke ikirrin basu.