Friday, December 5
Shadow

Muma Mun samu bayanan cewa lallai an shirya yiwa Shugaba Tinubu Juyin Mulki, kuma Sojojin da aka kama dalilin haka suna da yawa>>Inji Jaridar Punchng

Jaridar Punchng ta zama ta uku kenan data ruwaito cewa, an kama wasu sojoji da suka shirya yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu juyin Mulki.

Jaridar tace wata majiyar soji ta tabbatar mata da cewa kamen da kawa wasu sojoji sama da 16 na da alaka da shirin juyin Mulkin da suke shirin yiwa Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Jaridar Punchng ta kara da cewa wani janar ne ka jagoranar sojojin da ke shirin kifar da Gwamnatin Shugaba Tinubu wanda suka shirya yi ranar 1 ga watan October.

Saidai Hukumar sojojin Najeriya ta ce karyane babu wani shirin jurin mulki aka yiwa shugaba Tinubu.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Shugaban Najeriya, Bola Ahmad Tinubu yana tunanin kasar Faransa ce zata bashi mulki karo na 2 shiyasa yake musu biyayya>>Inji Shugaban Nijar

Jaridar Sahara reporters ce ta fara kawo labarin tace an kama sojoji 16 inda daga baya Premium times itama ta ce ta samu wanan rahoto inda tace an kama sojoji 20.

Rahoton jaridar Punchng yace amma kungiyar lauyoyi da sauran masu ruwa da tsaki sun yi Allah wadai da wannan yunkurin inda suka ce suna goyon bayan mulkin Dimokradiyya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *