Gwamnatin tarayya a hukance ta sanar da cire tallafin man fetur dana dala.
Ministan kudi, Wale Edun ne ya bayyana haka a wajan wani taro da aka yi da bankin Duniya a Abuja kan ci gaban da Najeriya take samu.
Ya kara da cewa tallafin ya lakumewa Najeriya kudaden da suka haura Naira Tiriliyan 10.
Ya bayyana cewa, zasu kawo saukin rayuwa da samun ayyukan yi ga ‘yan Najeriya ta hanyar samar da basukan gine-gine wadan za’a rika karba akan kudin ruwa da bai wuce kaso 1 cikin 100 ba.