‘
Yan majalisar kasar Amurka da suka kawo ziyara Najeriya wanda Riley Moore ya musu jagora sun ce sun gana da Kiristoci da aka yiwa cin zarafi a jihar Benue.

Sun ce sun gan su a matsayi na rashin tabbas wanda suka zargi Fulani da jefasu a ciki.
Riley yace ba zasu zuba ido suna ganin irin wannan abuba, dole zasu dauki mataki.
Yace ya ji labarai masu tayar da hankali da ‘yan Gudun Hijirar suka gaya masa wadanda ba zai taba mantawa dasu ba.