
Hukumar shirya jarabawar share fagen shiga Jami’a JAMB ta bayyana cewa, ta gano wata dabarar satar Amsa wadda dalibai ke karyar cewa su zabayane dan yin satar Amsar.
Shugaban hukumar, Professor Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan inda yace yawan daliban da suka yi rijistar Jarabawar a matsayin Zabaya sun yi yawa, shiyasa suka ce bari su yi bincike.
Yace da suka yi bincike sai suka gano ashe wata fasahar zamani ce aka zo da ita ta satar amsa wadda kuma idan daliban basu yi karyar cewa, su Zabaya bane ba za’a barsu su rubuta jarabawar ba.
Yace daga baya sun gano irin wadannan dalibai kuma ya jawo hankalin sauran daliban su kaucewa irin wannan lamari.