Friday, December 5
Shadow

Mun ji daɗin karramawar da ‘yan Najeriya suka mana>>Iyalin Buhari

Iyalin marigayi Muhammadu Buhari sun bayyana godiya da jin daɗinsu ga gwamnati da ‘yan Najeriya bisa karramawar da suka ce an yi wa tsohon shugaban ƙasar na Najeriya bayan rasuwarsa.

A ranar Talata ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya jagoranci binne Buhari a gidansa da ke garin Daura na jihar Katsina bayan ya rasu ranar Lahadi a birnin Landan sakamakon doguwar jinya.

Wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawun iyalin, ya wallafa yau Lahadi ta ce Mamman Daura ne ya wakilci iyalin wajen miƙa godiyar tasu.

“Mun yi farin ciki da irin kulawar da shugaba ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa da ministoci suka ba mu yayin jana’iza a nan Daura,” in ji Mamman Daura.

Karanta Wannan  Yaron Sojannan da muka lara dashi jiya sam bai da Kunya ga girman kan tsiya>>Inji Ministan Abuja, Nyesom Wike

“Muna matuƙar godiya ga shugaban ƙasa da ya ayyana ranar hutu da kuma sanya wa Jami’ar Maiduguri sunan Buhari. Muna kuma amfani da wannan damar domin gode wa dukkan ‘yan ƙasa da sauran ƙasashe da suka turo wakilci.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *