Monday, May 5
Shadow

Mun kusa ƙaddamar da haɗakar kawar da APC – Ƴan adawa

Manyan ƴan siyasar Najeriya da ke jagorantar shirin yin haɗaka tsakanin jam’iyyun hamayya domin tunkarar APC a zaɓen 2027, sun mayarwa ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP martani, a kan matsayar da gwamnonin suka ɗauka cewa ba su goyon bayan ƙulla duk wata haɗaka da za ta fitar da su daga PDP.

Gamayyar ƴan adawar da ta haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023 da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai da dai sauran ƴan siyasa, ta ce nan ba da jimawa ba za a sanar da ƙulla sabuwar haɗakar siyasa da za ta ceto Najeriya daga mulkin APC.

Ɗaya daga cikin jagororin tafiyar ƙulla sabuwar haɗakar siyasar ta Najeriya kuma tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa mai kula da shiyyar Arewa Maso Yamma, Salihu Lukman ya yi zargin cewa gwamnonin PDPn na sane cewa jam’iyyar su ta yi lalacewar da gyaran ta zai yi wahalar gaske, domin haka suke neman tallafawa jam’iyyar APC mai mulki da zummar ganin ƴan adawa ba su yi nasarar gabatar da ɗan takara mai nagarta ba a zaɓen 2027.

Karanta Wannan  Tinubu ya bai wa jihohi naira biliyan 108bn kan ambaliya da zaizayar ƙasa - Shettima

A ranar 20 ga watan Maris Alhaji Atiku Abubakar da Peter Obi da kuma magoya baya su suka sanar da shirin su na ƙulla wata gamayyar siyasa da za ta tunkari APC a zaɓen 2027 mai zuwa.

Sanarwar ta su ta janyo muhawara da tsokaci daga ɓangarori daban-daban.

Sai dai a ƙarshen wani taron da suka yi a ranar Litinin 15 ga watan Afirelu a garin Ibadan, gwamnonin jam’iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad sun yi watsi da yunƙurin kafa gamayyar suna jaddada cewa jam’iyyar suba za ta narke cikin wata gamayya ta daban ba.

A hirar sa da BBC, Malam Salihu Lukman ya gargaɗi gwamnonin na PDP da su sani cewa matakin na su wani yunƙuri ne na son ganin an tsayar da ɗan takara mara karfi, don taimaka wa shugaba Tinubu na jam’iyyar APC wajen samun nasara a zaben mai zuwa.

Karanta Wannan  Dansandan Najeriya ya Harbi Kansa Da Bìndìgà ya mùtù

Ya yi bayanin cewa a halin da Najeriya ke ciki yanzu, lokaci ne da ƴan siyasa za su taru waje guda ”Mu cire son zuciya, mu fahimci halin da ƙasar nan ke ciki, dole ne mu daure kowa ya zo a yi abin da ya kamata.”

”Ba daidai bane a ƙasa kamar Najeriya a ce baya ga jam’iyyar da take riƙe da gwamnati mai ci, duk sauran jam’iyyun sun shiga halin ƙaƙa nikayi, a zauna ana kallo har a kai gaɓar da za a yi zaɓe kuma a gaza tsayar da ƴan takara” in ji Salihu Lukman.

Ya ƙara da cewa abin da ya janyo tafiyar ta su ta neman kafa gangamin kenan kuma suna fatan cikin gwamnonin PDPn za a samu masu fahimta da za su shiga domin a yi tafiyar tare da su.

Dangane da dalilin da gwamnonin PDP suka bayar cewa su ba za su fita daga jam’iyyar su domin komawa cikin wata jam’iyya da ko kansila ba ta da shi kuwa, Malam Salihu Lukman ya ce ”Na farko tambayar ita ce ina jam’iyyar PDP take, ta taɓa ganin jam’iyyar da ta yi shekara biyu ta kasa yin meeting? A yanzu a halin da PDP da Labour party da NNPP suke, dukka suna cikin hatsarin da ba za su iya tsayar da ƴan takara ba.”

Karanta Wannan  Wata Sabuwa:Ana rade-radin an hana mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima shiga fadar shugaban kasa har hakan tasa fadar shugaban kasar yin magana

Ya tabbatar da cewa a ɓangaren su, shiri ya kusan kammaluwa kuma nan ba da jimawa ba za su sanar da kafa wata sabuwar haɗakar siyasa da za ta ƙumshi duk wani ɗan siyasa ”mai kishin ƙasa wanda yake son ganin Najeriya ta gyaru domin kafa jam’iyyar da za ta tsaya da ƙafafunta domin tsayar da ƴan takara masu nagarta”.

Masu sharhi dai na ci gaba da bayar da ra’ayoyi mabanbanta game da tasiri ko akasin haka da wannan sabuwar haɗaka ta ƴan adawa za ta iya yi a babban zaɓen Najeriya na 2027.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *